islamic sources

  1. home

  2. book

  3. Mu’assatu Shuhadah

Mu’assatu Shuhadah

Mu’assatu Shuhadah
4 (80%) 1 vote[s]
description book specs comment
GABATARWA

Ita dai wannan muassasah ta shuhada ta sami kafuwa ne tun ranar asabar 17 ga watan Rajab 1411 bayan hijirar Manzon Allah[SAWA] watau daidai da 1 ga watan Janairu 1992 a lokacin wani gangami da aka yi na yanuwa dake cikin wannan harka din a filin Babban Dodo Zaria. Mallam Ibrahim Zakzaky shine ya kaddamar da muassasar a lokacin jawabin sa daya gabatar.

Wannan abu kuwa ya biyo bayan wani mummunan kai hari da aka yiwa yan uwa ne a lokacin mulkin General Ibrahim Badamasi Babangida a garin Katsina inda da yawa daga cikin yanuwa suka jikkita aka kuma kama da yawa daga ciki sannan Mallam Abubakar Shehu Modomawa yayi shahada. Koda yake dama a can baya a shekara ta 1980 yan sanda sun taba bude wuta akan wani saurayi mai suna Muhammad a garin Bauchi wanda kuma yayi sanadiyyar rasuwar sa. A cikin jawaban na Mallam Ibrahinm Zakzaky ne ya nada wasu mutane a matsayin wadanda zasu rike ragamar wanna muassasah sannan kuma ya shata masu irin abubuwan da zasu aiwatar.

Kawo ya zuwa lokacin da aka hada wannan makalar akwai shahidai dari da takwas[108] cikin su akwai masu mata da yara wanda ya sanya aka sami marayu dari da ashirin da takwas [128] maza da mata.

MANUFOFIN WANNAN MUASSASAH

Babu shakka ita wannan muassasah har yanzu bata samu ta aiwatar da dukkanin abin data shata ba amma ta samu gabatar da wasu daga cikin ayyukan data sa a gaba,manufofin wannan muassasah sun hada da:

1 Bayar da taimako da tallabwa marayu wadanda iyayen su suka yi shahada suka bar su[tallabi na ma’ana dana rayuwa] koda yake dukkanin marayu ma sun shiga cikin wannan taimako,wadanda suka fada cikin bala’i, fursunoni da dai sauransu.

2 Assasawa da kuma gina makarantun firamare, gaba da firamare, jamio’i da dai sauran su.

3 Bada tallabi na kudi ga marayu masu son karatu [scholarship] a ko wanne matsayi na karatun su.

4 Kagowa da kuma tallabaw masu gudunar da wani bincike akan bangarorin da zai amfani mutane da yan adamtaka.

5 Bayar da cikakkiyar kariya ta lafiya tun daga abu mai sauki zuwa ga mafi girman matsayi na rashin lafiya a ko wanne lokaci aka bukata.

6 Samun filaye da kuma tanajin gina wuraren zama ga marayu da makarantun su.

7 Samar da kungiyoyi da wurare na buga mujallu da littafai da jaridu don amfanin jama’a.

8 Samar da kwararan kafofin watsa labari na zamani.

9 Samar da yanayi wanda zai bada dama wajen samar da musayan ra’ayoyi da wasu kungiyoyi daban daban ta hanyar ci gaba da fahimtar juna.

10 Shiryawa da kuma aiwatar da tarurruka na karawa juna ilmi, koyarwa a ciki da wajen kasar.

11 Shiryawa da gabatar da tara gudunmuwa daga jama’a, gwamanati ko kungiyoyi masu zaman kansu.

12 Sayen hannayren jari a kamafanoni da guraben kasuwanci daga kudaden da aka samu.

AYYUKAN WANNAN MUASSASH

Daga cikin ayyukan wannan harka baya ga shiryawa da kuma gabatar da taron shekara-shekara na”yaumu Shuhada” akwai kuma shirya tarurruka na karawa juna ilmi a baki dayan kasar. Ana taron shekara-shekara na ranar shuhada ne dai a ko wanne watan Rajab 17 gare shi inda akasarin yanuwa ke taruwa daga bangarori daban daban na kasar don sauraron jawaban da za’a gabatar. Galibi jagoran wannan harka Sheikh Ibrahim Zakzaky ne yake gabatar da jawabi a wannan taron.

Ana gabatar da shirye-shirye na ganin dukkanin marayu da aka bari sun sami kyakyawan karatu da wuraren kwanan su da dai sauran bukatocin su na yau da kullum.

Babu shakka irin halin da kasar ke ciki da kuma irin yadda har yanzun wannan muassash bata tsayu da kanta ba ya sanya wadannan abubuwa suna samiun dan cikas ba kamar yadda ake so ab.

KARIN BAYANI 

A duk lokacin da aka nemi karin bayani akan marayu da al’amurran su ana iya samu kai tsaye ta wannan muassasar.

ABIN DAKE HANNU

Kawo ya zuwa yanzun dai abin dake hannun wannan muassash yazo ne daga irin ribar da ake samu ta hanyar sayar da kayayyaki kamar su fina-finai, kasatoci na wake, da wasu littafai.

GUDUNMUWA

Ana iya bada gudunmuwa ta adireshin mu kamar haka No 1 Babban Dodo Zaria City, Nigeria.