islamic sources

  1. home

  2. book

  3. Mu’assasar Rasulul A’azam

Mu’assasar Rasulul A’azam

Mu’assasar Rasulul A’azam
3.1 (62.86%) 7 vote[s]
description book specs comment

Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai

Mu’assasar Rasulul A’azam (Sallallahu alaihi wa alihi) dake da mazauni a birnin Kano (Nigeria) wacce kuma take da rassa a sassa daban-daban na Nigeria, mu’assasar addinin Musulunci ce mai cin gashin-kai. Ta sami rejista da gwamnatin Tarayya ne a shekara ta 2005 miladiyya.

Bisa la’akari da bukatuwar da al’umma suke da ita na sanin hakikanin koyarwa ta addinin Musulunci a yanayi na gaba daya da kuma mazhabar Ahlulbaitin Manzon Allah (a.s) musamman bayan wani lokaci da aka dauka na yada farfaganda da kokarin shafa bakin fenti wa addini namu, don haka aka yi tunani assasa wannan mu’assasa ta Rasulul A’azam (s) a birnin Kano don biyan wannan bukata.

Alhamdu lillahi tun bayan assasa Mu’assasar, al’ummar musulmi a garuruwa a sassa daban-daban na Nigeria sun yi na’am da wannan ita da kuma rungumarta hannu bibbiyu da nufin aiki kafada-kafada don cimma wannan manufa, hakan kuwa ya biyo bayan irin laccocin da Mu’assasar ta dinga gabatarwa ne a wadannan sassa daban-daban.

Ya zuwa yanzu dai ‘yan’uwa a garuruwan Gombe, Bauchi, Katsina, Zaria, Sokoto, Maiduguri, Yola, Ilorin, Okene da dai sauransu wadanda tun da jimawa suke gudanar da ayyuka yada addinin Musulunci gwagwardon iyawansu, sun nuna aniyarsu na aiki kafada-kafada da wannan mu’assasar don cimma manufar da ake son cimmawa.

Kofar mu’assasar dai a bude take ga dukkan al’umma wadanda suke son aiki da ita ko kuma neman dukkan wani karin bayani kan mu’assasar da ayyukanta, kamar yadda kuma kofarta a bude take ga duk wani mai son taimakawa da ba da tasa gudummawa wajen cimma madaukakiyar manufar da mu’assasar take son cimmawa.

Manufar Mu’assasar Rasulul A’azam:

Ganin irin halin da duniyarmu ta yau ta shiga, na bukatar ayyukan wayar da kai a madadin yin amfani da karfin tuwo (wanda ya zamanto ruwan dare) wajen kokarin magance rikice rikice da matsalolin yau da kullum, sai muka ga ya zama dole mu taimaka wajen magance matsalolin dan Adam a wannan zamanin da duniya -wadda ta zama dan karamin gari daya- take samun sauye sauye, bisa karantarwar Ahlul-bait (AS), ta amfani da hanyoyi mabambanta da suke kunshe a:

1- Karantarwa:

Tun lokacin da aka kafa Mu’assasar Rasulul A’azam, mu’assasar ta dukufa wajen karantar da al’ummar musulmi musamman mabiya Ahlulbaiti (a.s) a mazaunin mu’assasar da ke unguwar Sani Mai Nagge, to amma bisa la’akari da karuwar dalibai da kuma tunanin gaba Mu’assasar, cikin ikon Allah da taimakon wasu ‘yan’uwa bugu da kari kuma kan hakkoki na shari’a da wasu ‘yan’uwa suke bayar ga wakilin jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran Ayatullah al-Uzma Sayyid Ali Khamene’i kan hakkokin shari’a, wato Sheikh Muhammad Nur Dass, ta sanya tubalin ginin Makarantar Baqirul Ulum don ci gaba da karantarwa da kuma gudanar da wasu ayyuka na cibiya a wajen.

Baya ga karantarwar da ake yi mazaunin mu’assasar, akwai kuma wasu karantarwar da ake yi a wasu sassa na garin Kano.

Har ila yau baya ga garin Kano, a kowani wata, malaman mu’assasar suka tafi tabligh zuwa garuruwa daban-daban da suka hada da Bauchi, Zaria, Katsina, Danbatta, Gombe da sauransu, inda a wannan lokaci a kan karantar da ‘yan’uwa bangarori daban-daban na addininsu.

2- Talife-Talife da Tarjama:

Baya ga karantarwa, Mu’assasar Rasulul A’azam (s) ta dukufa wajen rubuta da kuma tarjama wasu muhimman littafa don amfanin al’umma da kuma cimma manufarta ta wayar da kan al’umma da koyar da su koyarwar Musulunci na hakika.

Ya zuwa yanzu mu’assasar ta rubuta da tarjama littafa kamar su: Tafsir Rabi’ul Muminin da Sheikh Muhammad Nur Dass, Sheikh Bashir Lawal da Marigayi Malam Awwal Tal’udi suka wallafa, sai kuma littafin Tambayoyi da Amsoshinsu (Al-Istifta’at) da ya kumshi fatawoyin Jagora Ayatullah al-Uzma Sayyid Ali Khamene’i da Sheikh Muhammad Nur Dass, marigayi Malam Awwal Tal’udi da Malam Awwal Bauchi suka tarjama, sai kuma Littafin Shi’a da Akidojinta Me Zai Hana Hadin Kai da Sheik Saleh Zaria ya buga da kuma fassarawa, sai kuma Tsinkaya Cikin Tarihi (da ya kumshin tarihin Manzon Allah da Ahlulbaitinsa (a.s) da Sheikh Saleh Zaria da Malam Awwal Bauchi suka fassara, da sauransu da za a iya ganinsu a bangaren littafanmu.

Ga wasu daga cikin hotunan littafan:
3- Gabatar da Laccoci:

Baya ga karantarwa da kuma talifi da tarjama, Mu’assasar Rasulul A’azam (s) tana gudanar da tarurrukan gabatar da wa’azi da laccoci a mazaunin mu’assasar da ke Kano da kuma sauran garuruwa daban-daban na Nigeria a lokuta bukukuwa haihuwar Manzon Allah (s) da Imaman Ahlulbaiti (a.s) ko kuma lokacin wafati da shahadarsu, kamar yadda kuma take gabatar da irin wadannan tarurruka a wasu lokuta masu muhimmancin gaske ga mabiya Ahlulbaiti (a.s), misalin lokacin juyayin Ashura na shahahar Imam Husaini (a.s) da mabiyansa, da kuma lokacin Eid al-Ghadir, wato lokacin da Manzon Allah (s) ya zaba wa al’ummarsa wanda zai kasance shugabansu a bayansa, da dai sauran bukukuwa na farin ciki da bakin da ya samu Ahlulbaiti (a.s).

Mu’assasar ta kan gudanar da hakan ne ta hanyar tura wasu daga cikin masu wa’azinta zuwa wadannan garuruwa, inda ake gudanar da laccoci da kuma amsa tambayoyin al’umma.

Kofar Mu’assasar dai a bude yake ga duk wanda ke son ba da gudummawarsa.

 

Mu’assasar Rasulul A’azam (s) ta yi amanna da cewa wadannan hanyoyi da aka ambata a sama, wato karantarwa, talife-talife da tarjamar littafa da kuma gudanar da tarurrukan wa’azi da laccoci suna daga cikin manyan hanyoyin da za a iya bi don wayar da kan al’umma din da sanya su kan mikakkiyar hanya da za ta zamanto musu alheri da duniya da kuma lahira.

Tuni dai Mu’assasar ta dukufa wajen aiwatar da kowani guda daga cikin wadannan hanyoyi da aka lissafa a sama, inda a halin yanzu mu’assasar tana nan tana kan gina makaranta inda za ta dinga karantar da dalibai da aka sanya mata suna Makarantar Baqirul Ulum da ke nan birnin Kano, wacce kuma take da adireshi na email kamar haka [email protected].

A bangaren talife-talife da tarjaman littafa kuwa, mu’assasar ta buga da tarjama littafa daban-daban da suka shafi bangarori daban-daban na rayuwa da za a iya ganinsu ta nan, kuma ana iya neman karin bayani kan wannan bangare ta adireshin email kamar haka [email protected].

A bangare wa’azuzzuka da laccoci kuwa mu’assasar ta gudanar kuma tana ci gaba da gudanar da laccoci da tarurrukan wa’azi a garuruwa daban-daban na Nigeria musamman a lokutan bukukuwan haihuwa ko kuma shahadar Ahlulbaiti (a.s) da dai sauran bukukuwa, baya ga laccocin da malaman mu’assasar suke gudanarwa wata-wata a garuruwa da kuma a lokacin azumin Ramalana. Ana iya neman karin bayani kan wannan bangare ta adireshin email kamar haka [email protected].

Masu tafiyar da wannan mu’assasar sun hada da:

1: Sheikh Nur Dass

2: Sheikh Saleh Zariya

3: Sheikh Bashir Lawal

Ana iya samun mu a adiresoshinmu kamar haka:

Tel: +234-064945916

Email: [email protected]