islamic sources

  1. home

  2. book

  3. Madarasa

Madarasa

Rate this post
description book specs comment

Takaitaccen bayani kan Madrasa


GABATARWA

Godiya ta tabbata ga Allah wanda ya hallici mutum kuma ya koyar da shi da alkalami.Amincin Allah ta albarkatun sa su tabbata ga fiyayyen halitta Muhammad dan Abdullah [SAWA] iyalen gidan sa tsarkaka da sahabban sa na gargaru, da duk wadanda suka bi tafarkin su tare da gwagwarmaya don tabbatar da daukakan Allah adoron kasa. Allah ya dada tsira ga limamin wannan lokacin sahibuzzaman Imam Mahdi Allah ya gaggauta bayyanar sa, amin.

Cibiyar yada ilmi ta Fudiyya ta kafu ne tun shekara ta 2002. Ita dai wannan cibiya wadda take can kan titin Kano-Kaduna kusa da mahadar hanyar Dan magaji da Wusasa, ta kunshi dakunan kwana guda uku da shaguna kamar guda biyar. Wannan Harka ta mallaki wannan wuri ne ta hanyar irin gudunmuwar da aka saba karba daga hannun yanuwa dake cikin harkar. Kuma muna masu godiya ga Allah ta’ala wanda ya bamu shugaba mai dogon hangen nesa da ya sanya mana ruhin dogaro da kai tun farkon wannan al’amari.Sai dai kamar yadda wadanda suka san wajen zasu iya gani bayan an mallaki wannan gida anyi masa wasu gyare-gyare an fitar da wuraren kama ruwa na maza dana mata dadai sauran su. Don haka a yanzu ana iya cewa wannan cibiya tana da wurare kamar haka: Dakin karatu [Library], Dakin radio ta Telbijin inda ake iya gani da kuma jin labarai na mahalli dana duniya baki daya, shagon saida kayayyakin masarufi, da dakin kwamfuta wanda yake hade da dakin karatu. Sannan daya daga cikin banagren ginin an maida shi dakin saukan baki bayan an yi masa wasu kwaskwarima.

Tun farko dai ya kasance babban manufar jagoran wannan harka Mallam Ibrahim Yakub Zakzaky game da wannan cibiya shine samar da wata MADARASA wadda zamu iya  gani a sauran kasashe na duniya daban-daban. Kuma kamar yadda Mallam din ya sha nanatawa ita makaranta ya kamata ne ta kasanceta hado komai da komai a hakikanin ma’anar makaranta. Watau ya zama tana da dakunan kwanan dalibai, azuzuwa, dakin cin abinci, dakin ajiya [store], shaguna da dai sauran su. Ta yadda shi dalibi in ya riga ya shiga makaranta to zai ma iya yin kwanaki masu yawa ba tare da ya nemi fita don wata bukata tashi ba.

Duk da cewa har yanzun ba’a sami damar hakkaka wannan buri ba amma dai al’amarin gina makaranata wadda mallam din yake nufi bata fita daga tunanin wannan harka ba, domin kuwa yanzu haka ma an riga na sai wani fili wanda kuma an saya ne da wannan manufa din, in sha Allah kuma nan da lokaci kankani za’a ga wannan abu ya tabbata.

GAME DA FUDIYYA

Wannan suna fudiyyah an dauko shi ne daga kalmar fodio wanda a harshen fulfulde yake nufin masani. Wannan kuma wani lakabi ne da aka baiwa mujaddadi Shehu Usman dan Fodio [yardan Allah ta tabbata a gare shi] kowa ya san yadda shi wannan bawan Allah tare da jama’arsa suka yi yaki kuma suka kai har ga nasara wanda albarkan wannan abu ne ya sanya wannan yanki ya zama abin da ya zama a yanzu. To bayan cin nasarar da Shehu yayi ya baiwa wasu daga cikin almajiran sa tutoci kuma ya nada su a birane daban-daban domin ci gaba da karantarwa irin ta addinin musulunci, kuma daga wannan ne wannan harka ta sami wannan kyakyawan suna da fatan zata sami albarkar wannan kyakyawan aiki.

Zamani ya sahida irin ayyukan da Shehu da almajiran sa kamar su Shehu Abdullahi da su Muhammadu Bello suka yi tun daga abin da ya shafi littafan fikihu don koyar da shari’ah kama ya zuwasu littafai da suka wallafa kan tafiyar da mulki da abin da ya shafi tattalin arziki da dai sauransu. Ba zamu manta da liattafai irin su dhiya’ul hukkam, Bayan wujubul hijra da dai sauran su wadanda wadannan bayin Allah suka wallafa ba. Abin ban takaici shine irin yadda ya zama a yanzu wanna koyarwa ta Shehu ta kasance abiun da kawai aka sani cikin tarihi domin kuwa an riga an bar turba ta Shehu tun bayan bayyanar turawan mulkin mallaka.

To amma cikin yaddan Allah farawan wannan harka ya zama kamar wani tobali ne na kokarin ganin an dawo kan wancan turba mai tsarki ta daular Usmaniyya wadda zata baiwa mutane mutuncin su da suka rasa. To shi jagoran wannan harka Mallam Ibrahim Zakzaky sai yaga tun da manufar mu ita ce tabbatar da adalci da hakimiyya din Allah a bayan kasa a kalla a wannan nahiya da muka samu kan mu kuma shine irin aikin da Shehu yazo yayi sai ya sanya wannan suna Fudiyya ga dukkanin makarantun wannan harka. A halin da ake ciki yanzu akwai makarantu a kimanin garuruwa dari biyu na baki dayan kasar. Don haka wannan ya bada dama ta yadda a ko wacce Da’ira ta yanuwa akwai ko dai Firamare ko kuwaIslamiyya don koyar da manyan mutane, wadanda kuma dukkanin su suna bin tsarin darasi iri daya.

 

AYYUKAN DA AKE YI A WANNA CIBIYA.   

Ana gabatar da ayyuka daban -daban a wannan cibiya wadanda suka hada har da na mako-mako, ko mako bibbiyu, ko na wata-wata. Akwai Tafsirin Al-kurani mai girma wanda Jagoran wannan harka Mallam Ibarhim Zakzaky yake yi dukkanin laraba da yamma watau 4:00-6:00, Addu’oi wanda ake yi dukkanin ranakunlaraba da jummu’a da daddare, taron karawa juna ilmi wanda ake yi daga bangaren maza da mata, tarurrukan yanuwa Hurras da dai sauran su.

Daurah watau wani dan kos na gajeren lokaci da yanuwa na harkan suke yi da nufin inganta ilmin su na bangarori daban-daban, tarurrukan hukumar kula da lafiyar jama’a [Medical Team] da dai sauran abubuwa da dama.