islamic sources

  1. home

  2. book

  3. GUDUMMUWAR MACE

GUDUMMUWAR MACE

GUDUMMUWAR MACE

download

    Download

Rate this post
description book specs comment

“Muminai maza da Muminai mata kuwa masoya juna ne; suna horo da aikata alheri suna kuma hani da mummunan aiki..”Surar Taubati, 9:71.
“Ya ku mutane, hakika Mu Muka halicce ku daga namiji da mace, muka kuma sanya ku al’ummu da kabilu (dabam-dabam) don ku san juna, hakika mafi girmanku a wurin Allah shi ne wanda ya fi ku tsoron Allah…”Surar Hujarati, 49:13.
Yabo da godiya sun tabbata ga Allah Ubangijin talikai.Tsira da aminci su tabbata ga shugabanmu Muhammadu da tsarkaka daga lyalansa da zababbu daga Sahabbansa.
Zamantakewar dan Adam ba ta taba zama a wata rana cikin wadatuwa daga mace ba, alhali kuwa ita ke matsayin rabin samuwarsa ko ma fiye da haka. Duk wanda ya nutsa cikin zurfin tarihin dan Adam, zai ga cewa, hatta a lokutan da suka fi koyaushe ci baya, mace na da wata babbar gudummawa, duk kuwa da cewa wannan gudummawa ta faku daga gannai.
Idan har wayewar zamani ta fuskanci yin ta’akidi a kan gudummawar mace (a rayuwa) da ta da yekuwar kiyaye hakkokinta, duk da cewa na bayyane ne kawai, to Musulunci tun farkon bayyanarsa, ya yi kira kan cewa mace ta taka rawarta a rayuwa, kuma ta dauki nauyin da ya hau kanta wajen ginin wayewar bil-Adama. Allah Madaukaki Ya ce:­
“Sai Ubangijinsu Ya amsa musu (cewa): `Hakika Ni ba zan tozarta aikin wani mai aiki ba daga cikinsu, namiji ne ko mace’, sashinku daga sashi yake…” Surar AIi-Imrana, 3:165. Idan har mace a lokacin jahiliyya ta kasance wani kashi da aka yi watsi da shi wanda kuma ya fada karkashin tsiraici da kaskancin matsayi, to a cikin zamantakewar Musulunci ta dawo ta zama mutum wadda ke da abin koyi ga sauran muminai. Tarihin Musulunci ya shaida wasu lokuta masu muhimmanci na wasu fitattun mata, kamar Uwar Muminai Khadija, da shugabar matan duniya Fadimatu (a.s.).
Wata kila karnonin karshe-karshen nan, saboda jahilcin da ya bayyana cikin wasu garuruwan Musulmi kamar sauran garuruwan duniya, sun shaida wani nau’i na kangiya ga mace daga irin tasirin ta na dabi’a, da hardiya ga tafiyarta na cika; abin da ke sanya tilascin yunkurar wa da tunatar da tunane-tunanen Musulunci da suka ta’allaka da ita, domin kuwa sanya mace a fagen da ya dace da ita cikin rayuwa, yana da babbar gudummawa cikin yunkurin al’umma da bunkasarta.
Babu shakka kan cewa wannan gudummawa ya saba da hakikanin yadda mace ke rayuwa a al’ummun da ke bin abin duniya na zahiri, wandanda suka janye wa mace karamarta da mutuncinta, suka so ta zama na’urar tallace-tallace a kafafan watsa labarai, kuma kayan wasa wadda masu kudi ke amfani da ita bisa son zuciyoyinsu; a karshe sai mace ta rasa matancinta, uwartakarta, daukakar tunaninta da taushin ranta, ba ta girbe komai daga hakan ma face ta’addanci, yin watsi da ita a gefe, yanke kauna, wahalhalu da shigar iyali cikin halin kaico da wastewa.
Binciken da ke hannunka, ya kai mai karatu, wata ‘yar sassarfa ce a kan gudummawar mace da ayyukanta cikin al’umma bisa tunanin Musulunci. Muna fatan zai sami lura da muhimmanci daga gare ka.
Dukka godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai.