islamic sources

  1. home

  2. book

  3. Alhassanain (A.S)

Alhassanain (A.S)

Alhassanain (A.S)
4 (80%) 1 vote[s]
description book specs comment

 

Da Sunnan Allah Mai Rahama Mai Jin Qai

 

Shafin Sayet Din Imamai alhassanain (A.S) Na Wayarwa Da Tunanin Musulunci

 

Shafi ne da ya himmantu da tace da gyara manyan littattafan musulunci da fikirarsa ta asali da yada su, wadanda suka zo daga ma’aikin Allah (s.a.w) ko Ahlul Bait (a.s) da sahabbai (r) ko kuma wadanda alkaluman malaman wannan al’umma na yanzu da na da suka rubuta da wacce marubuta suka wallafa.

Hadafinmu shi ne mu yada musulunci kamar yadda ya zo tun asali da gyara al’adun al’ummarmu ta musulunci da ci gabanta, da kuma sanya madogarar asali na littattafai da karatuttuka na ilimi a hannun masu so da masu bibiya daga ma’abota wayewa da bincike a intanet.

Shafin yana kunshe da littattafa masu yawa a cikin fagage mabambanta na ilimomi masu yawa na musulunci, kuma yana da rassa da suka shafi bayanai mafi girman janibobin ilimi da wayewa, da kuma littattafai masu dama da karatuttuka shiryayyu domin budawa da gurzawa.

Sannan hada da wani bangare da sayet din yake da shi na wasiku da sakonnin zaman tare, da kuma mujallu masu yawa na ilimi mai dauke da sunanyen shahararrun marubuta ma’abota ilimi da kwarewa, tare da laburare da bayanan sauti da suke kunshe cikin karatu da tilawa iri-iri ta Kur’ani mai girma, da laccocin al’adu da wayewa, da darussan karatu na makarantun addini na Hauzozi, da addu’o’i da ziyarori, da wakokin madahu da yabon Annabi (s.a.w) da alayensa (a.s).

Wannan duka tare da cewa wannan shafin yana da wani bangare da ya kebanta domin su ma masu dubawa su bayar da tasu gudummuwar da mahangarsu kan abin da suke gani da ya cancanci tattauna da bincike.

Shafinmu ya kwadaitu matuka domin ci gaba da sanya sababbin bayanai a jere, kuma kofarsa tana bude ga dukkan masu ra’ayoyi a gyara da zasu bayar da gudummuwa wajan ganin an samu ci gaban iliminmu domin yin hidima ga musulunci da wayewarsa mai wadata. Abin da muke shelantawa a nan shi ne fadin nan na madaukaki: “Kuma Ka ce ku yi aiki, da sannu Allah da manzonsa da muminai zasu ga aikinku”. Tauba: 105. Allah ne mai shiryarwa ga tafarkin daidai.

an bude wannan sitin da yarurruka guda 14 wanda sun hada da: عربى, فارسى, اردو, English, Français, TurkishIndonesianHausa, Swahili, Azəri, Русский中文, हिन्दी, ไทยแลนด์.