islamic sources

Islamic Sources
Dakin Karatu na Yanar Gizo-Gizo Mafi girma a Duniyar Musulunci .
Waje ne da yake dauke da Littafai na Musulunci tun daga farkon Musulunci.
Akin wannan dakin karatun shi ne tattara koyarwar Manzon (s) Da kuma koyarwar shuwagabannin Musulunci, wanda suka biyo bayan shi. Haka nan kuma yana gabatar da binciken da masu nazari a kan Musulunci suka yi a kan Musulunci.
Wannan dakin karatun yana dauke da sama da yaruka 30, wanda ana amfani da su a duniya. Kowanne yare daga cikin wannan yaruka da aka ambata akwai masu magana da yaran sama da mutum miliyan 5.
Tattara Littafai da kuma shirya su da kuma tsarasu babi-babi da saukakawa mai karatu kaiwa ga abin da littafai suke dauke da shi yasa wannan dakin karatu ya zama abin karba wajan masu ziyarar shi.
MANUFAR ISLAMIC SOURCES:
1- Samar da dakin karatun da yake dauke da littafan Musulunci a kowanne bangare na Musulunci tare da kiyaye hadin kan al’ummar Musulmi da kusantar juna a tsakaninsu.
2- Gabatar da abin da littafan Musulunci suka kunsa tare da yarukan duniya, wadanda ake amfani da su.
3- Saukakawa wajan bincike ga masu bincike a kan Addinin Musulunci da sauran masu magana da wadannan yaruka.
4- Gabatar da Littafan Musulunci na asali masu daraja ta daya a wannan bangare.
5- Gabatar da Musuluncin gaskiya kamar yadda manzon tsira ya koyar da shi domin kare Musulunci daga makiyan shi, wanda koda yaushe suke batawa Musulunci suna.
ABUBUWAN DA LITTAFAN SUKA KEBANTA DA SHI.
Kafin a saka kowanne Littafi a cikin wannan dakin karatu sai masana musu kwarewa sun duba littafi sun tabbatar babu wani matsala a ciki saboda kiyaye hadin kan Musulmi da kiyaye iyakar Musulunci.
Mai karatu zai iya dauka (sauke) kowanne littafi da mukalolin da yake bukata a cikin wannan dakin karatu cikin sauki ba tare da wani sharadi ba.
An tsara gaba dayan abin da dakin karatun yake dauke da shi zuwa manyan-manyan batutuwa guda takwas, kuma anyi shi cikin babi 80 tare da yi masa unwani kamar yadda musulunci ya raba shi.
Mai bincike zai iya yin bincike a zamanance tare da zabar mawallafin littafi ko Madabba’a ko mai tarjama. An yi amfani da tsari mafi inganci domin sauqaqawa masu ziyarar wannan dakin karatu da kuma kyautata jin dadinsu.
Sabunta tsare-tsaren dakin karatun a kan lokaci.
DANGANE DA LITTAFAN:
Wannan bangare yana dauke da makalolin Musulunci mafi inganci, kuma yana bawa mai karatu da mai bincike damar samun Masdarinta saboda samun sauki samun ta lokacin da suka ziyarce shi.

 

MUJALLOLI.
Wannan bangaren taska ne na ilmi wanda yake dauke da mujalloli masu yawa, wanda aka rubuta su a kan Musulunci, kuma duk da amfani da yake tattare da shi amma masu ziyartar shi sun yi karanci.