islamic sources

Yau Lahadi biyu ga watan Janairu ita ce ranar Mazhabobi na Duniya, don haka muka ga ya dace mu yi duba game da Mazhabobin Musulunci a takaice.

Sabanin dake tsakanin Mazhabobin Musulunci yana komawa ne ya zuwa bahasosi biyu ko dai bahasin Akida ko kuma na Fikihu.

Rarrabuwa ta bangaren Akida, sabanin ya samo asali ne tun zamanin Manzon Allah(s.a.w).

A nan akwai manyan kungiyoyi guda biyu. Na farko sune mabiya Ahlussunna wadanda ke daukaka wani sashe daga cikin Sahabbai da ganin cewa su ne suka cancanci shugabanci bayan Manzon Allah kuma su ne za a bi bayan Manzon Allah. Na biyu kuma sune mabiya iyalan gidan Manzon Allah. Sannan kuma su wadannan sun yi imani da cewa akwai nassi da aka ruwaito daga Manzo Allah(s.a.w) na cewa Ali Dan Abi Dalib shi ne shugaba kuma  khalifa bayan Manzon Allah da kuma ‘Ya ‘yansa in da yake cewa” Khalifofi a bayana goma sha biyu ne”, don haka ma ake kiransu da mabiya Imamai sha biyu.

 

Amma sabani tsakanin Musulmi ta bangaren Fikihu sun kasu zuwa kaso biyar ne, kamar yadda babban Shehi a Jami’ar Alazhar Mahmud Shaltut ya fada cewa riko da daya daga cikin wadannan Mazhabobi ya halasta. Sune: Malikiyya,Hanafiyya,Shafi’iyya,Hambaliyya da Mazhabin Ahlul bait.

 

Mazhabar Malikiyya

Ana jingina wannan Mazhaba zuwa ga Baban Abdullah Anas Dan Malik Dan Baban Aamir Al-Asbahi. An haife shi a garin Madina shekara ta 92 bayan Hijira. Ya fara karatu yana dan karami, yayi karatu a wajen Nafi’u wanda yake almajiri ne a wajen Abdullahi Dan Umar da sauran su. Ya rasu a Madina a shekara ta 179 bayan Hijira kuma an bizne shi a Baki’a.

 

 

Mazhabar Hanafiyya

Ana jingina wannan mazhaba zuwa ga Imam Abu Hanifa Nu’uman Dan Sabit Dan Al-Tamimi Al-Kufi. An haife shi a shekara ta 80 bayan Hijira. Ya kasance Fakihi, yayi aiki da kiyasi a wajen fitar da hukunce-hukuncen Fikihu da kuma gwama su da nassosi don fadada iliminsa na Fikihu. Sarki Mansur ya neme shi da zama Alkali sai ya ki karba tsoron kada ya zalunci wani, saboda kin amincewarsa ya sa aka kulle shi a kurkuku. Ya rasu shekara ta 150 bayan Hijira.

 

Mazhabar Shafi’iyya

Ana jigina wannan Mazhabar zuwa ga Imam Abu Abdullah Muhammad Dan Idris Al-Karashi Al-Shafi’i. Ya kasance maraya, kuma an haife shi a shekara ta 150 bayan Hijira a Gaza daga baya ya koma wurin mahaifiyarshi a garin Makka, a lokacin yana da shera biyu. Ya rasu a shekara ta 204 bayan Hijira yana dan shekara hamsin Da hudu.

 

Mazhabar Hambaliyya

Ana jingina wannan Mazhaba zuwa ga Imam Ahmad Dan Hambal Dan Hilal Al-Zahli Al-Shaibani. An haife shi a Iraki a Bagdad shekara ta 164 bayan Hijira. Ya yi zirzirga tsakanin Hijaz da Damashk da Yaman don neman ilimi mai yawa. Kuma ya kasance daya daga cikin manyan almajiran Shafi’i a Bagdad har ya kai matsayin mujtahidi, kuma ya haddace Hadisan Manzon Allah da dama da mas’alolin Fikihu a wajen malaminsa. Kuma ya wallafa littattafai da yawa daga ciki akwai ”Musnad”.

 

Mazhabar Ahlul Bait ko Jafariyya

Ana jingina wannan Mazhaba zuwa ga Abu Abdullah Ja’afar Dan Muhammad Al-Bakir Dan Ali Zainul Al-Abidin Dan Hussain Dan Ali Dan Abi Dalib mijin ‘Yar Manzon Allah Sayyida Fatima shugaban matan Duniya. An haife shi a shekara ta 83 bayan Hijira kuma shi ne limami na  shida cikin jerin limamai goma sha biyu na Shi’a. Yana da ‘ya’ya goma maza bakwai mata uku. Ya kasance mai yawan ilimi da takatsantsan, kuma ya yi wallafe wallafe da dama, sannan yana da almajirai fiye da dubu hudu a bangaren Hadisi, Fikihu, Tafsiri da sauransu. Ya zauna a Madina kuma ya shiga Iraki ya dade a cikin ta. Imam ya rasu a shekara ta goma na mulkin Sarki Mansur a 148 bayan Hijira kuma an bizne ne shi a Baki’a.